Isa ga babban shafi

An tsaurara tsaro a wasu jihohin kudancin Najeriya saboda masu neman kasar Yarbawa

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a daukacin gine-ginen gwamnati da ke faɗin jihar.

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya Photo: Reuters
Talla

Wannan dai ya biyo bayan mamayar da wasu gungun matasa masu neman kafuwar kasar Yarbawa suka yi wa Sakateriyar gwamnatin jihar Oyo dauke da muggan makamai.

Tun a ranar Lahadi ne, rundunar ‘yan sandan jihar ta Oyo ta sanar da cafke mutane 20 kan harin da aka kai wa rukunin ma’aikatun gwamnatin jihar.

Rundunar ta kuma kwace makamai da dama a hannun matasan da suka hada da bindigogi da alburusai da kuma adduna.

Tuni dai shugaban kungiyar masu fafutukar neman kafuwar kasar Yarbawa, Sunday Igboho da a baya ya taba tserewa zuwa Jamhuriyar Benin bayan tuhumarsa da cin amanar kasa, yace babu hannunsa a wannan lamari.

A halin da ake ciki yanzu daukacin gwamnonin da ke yankin Kudu maso gabshin Najeriya sun bukaci daukar matakan dakile ire-iren wadannan kungiyoyi da ke kawo tsaiko ga zaman lafiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.