Isa ga babban shafi

Najeriya ta ƙaddamar da rigakafin cutar sanƙarau irin sa na farko a duniya.

Najeriya ta kaddamar da allurar riga kafin cutar sankarau, wacce za'ayi amfani da ita ita wajen kawar da cutar a yankunan da ke fama da wannan cuta ba lahira. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana riga kafin a matsayi ta farko a ire-iren alluran da ake samarwa da zummar yakar cutar a duniya.

Maiduguri: Daya daga cikin kananan yara a tarayyar Najeriya da ta kamu da cutar Sankarau da ke bulla a lokacin yanayi na zafi.
Maiduguri: Daya daga cikin kananan yara a tarayyar Najeriya da ta kamu da cutar Sankarau da ke bulla a lokacin yanayi na zafi. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rigakafin zai kare mutane daga nau'uka biyar na kwayar cutar sankarau da ake kira meningococcus bacteria , a cewar darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Ƙungiyar Gavi da ke fafutukar yin rigakafin cututtuka a duniya ce ta dauki nauyin yin rigakafin daga ranar 25 zuwa 28 ga watan Maris da zummar yi wa fiye da mutum miliyan daya ƴan shekara daya zuwa 29 allurar.

Nijeriya ta ƙaddaramar da wani nau'i na rigakafin cutar sanƙarau mai suna Men5CV da zai samar da sauyi matuka, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce shi ne na farko a duniya.

WHO ta ci gaba da cewa Wannan shiri da Nijeriya ta ƙaddamar ya ƙara kusantowa da su wajen cim ma burin da suke dashi na kawar da sanƙarau daga nan zuwa shekarar 2030.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.