Isa ga babban shafi

Duk da tsadar lantarki an gaza wadata 'yan Najeriya da hasken wutar

Mako guda bayan karin kudin wuta a wasu sassan Najeriya kamfanonin rarraba wutar sun gaza bayar da wutar da suka yi alkawari ta tsawon sa’o’I 20 zuwa 24.

Turakun wutar lantarki a Najeriya.
Turakun wutar lantarki a Najeriya. © Ventures Africa
Talla

Rahotanni sun ce cikin mako daya tak, kamfanonin su wallafa takardar ban hakuri ga jama’ar da ke zaune a yankunan da ake bayar da wutar ta tsahon sa’oi 20 zuwa 24 har sau 37 a shafukan su na Internet.

Gwamnatin Najeriya dai ta yi karin kudin wuta a wasu sassa daga naira 68 zuwa naira 225, wato ninkin sama da kaso 300 kenan.

To sai dai kuma tun kafin karin yaje ko ina aka fara samun matsaloli, daga bangaren kamfanonin rarraba wutar lantarkin a inda suka kasa cika alkawarin samar da wutar awanni 20 zuwa 24 kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.