Isa ga babban shafi

Muna rayuwa cike da fargabar yiwuwar rasa aikinmu- Ma'aikatan CBN

Tarin ma’aikatan babban bankin Najeriya CBN na rayuwa cike da zullumin yiwuwar rasa aikinsu kowanne lokaci lura da yadda sabon gwamnan bankin Dr Olayemi Cardoso ke ci gaba da korar dimbin ma’aikata daga kowanne sashe na bankin.

Ginin Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja.
Ginin Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Wasu ma’aikatan CBN da jaridar Daily Trust ta zanta da su, sun bayyana cewa suna cike da zullumi sakamkon yadda ake yi musu dauki ɗai-ɗai ba tare da ragawa kowanne sashe ba.

A cewar Daily Trust ma’aikatan sun sake shiga zullumi ne bayan korar karin ma’aikata 50 a Litinin din makon nan, adadin da ya mayar da jumullar ma’aitana da Dr Cardoso ya kora cikin kasa da kwanaki 20 zuwa ma’aikata 117.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan ma’aikata sun kunshi wadanda suka fito daga dukkanin sassan da ke karkashin bankin na CBN 29.

Korar ma’aikatan dai ta fi shafar masu manyan mukamai da suka kunshi manyan daraktoci da kanana sai kuma mataimakan daraktoci manajoji manya da kanana yayinda a baya-bayan nan korar ta fara hadawa har da kananun ma’aikata.

Wasu bayanai na daban sun ce hatta sashen kula da lafiyar ma’aikatan bankin sai da sabon gwamnan na CBN ya kori ma’aikata daga cikinsa wanda ke nuna babu sashen da zai tsira a guwuwar ta korar ma’aikata.

Tun bayan nadinsa mukamin Dr Olayemi Cardoso ya samar da sabbin tsare-tsare a wani yunkuri da ya ce zai farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya jima a cikin yanayi na mashasshara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.