Isa ga babban shafi

Babban Bankin Najeriya ya sake korar ma'aikata 40

Mutane 40 ne Babban Bankin Najeriya CBN ya sake sallama daga bakin aiki, mafi yawancinsu na aiki ne a sashin habaka harkokin kudi, a wani mataki na kawo sauye-sauyen da bankin ke yi.

Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja.
Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

A cewar wani bincike da jaridar Daily Trust da ake wallafa a kasar, a yammacin ranar Juma’ar da ta gabata ne bankin ya fidda sunayen mutanen, lamarin da ya sanya aka samu karancin bayanan wadanda abin ya shafa, duk da dai wakilin jaridar ya ce akwai sunan Musa Zgabawa Bulus, mataimakin daraktar sashin kula da kaddarorin amsar lamuni ga kanana da matsakaitan masana’antu.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa akwai masu mukamin mukaddashin darakta da kuma mataimakan darakta 22 daga sashin habaka harkokin kudi na bankin da lamarin ya shafa, sannan ragowar 18 din sun fito ne daga bangaren kiwon lafiya da kuma cinikayya.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya, akwai kimanin ma’aikatan bankin 27 da aka fara sallama daga bakin aiki, duk da cewa a yanzu haka wasu bayanai na cewar akwai wasu da za a sallama a cikin kwanaki masu zuwa.

Daga cikin mutanen da aka fara sallaman, akwai daraktoci 8 da mukaddashin daraktoci 10 da mataimakan daraktoci 5 sai wasu manyan manajoji 4.

Da wannan kora da Babban Bankin na Najeriya CBN yayi a yanzu, adadin wadanda aka sallama a karkashin jagorancin gwamnan bankin Olayemi Cardoso ya kai 67.

Jaridar Daily Trust ta ce duk kokarin da ta yi donjin tabakin daraktar yada labarai ta bankin Hakama Sidi Ali abin yaci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.