Isa ga babban shafi

Jami'in tsaro a Zamfara ya bindige wani mutum har lahira a yayin Sallar Idi

An samu rudani a jihar Zamfara da  ke arewa maso yammacin Najeriya a wannan Laraba, a bayan da wani jami’in tsaro, bisa kuskure ya bindige wani mutum da ke ibada a Sallar Idi har lahira.

Rudanin da ya samu bayan da wai jami'in tsaro ya kashe wani mutum a filin idi.
Rudanin da ya samu bayan da wai jami'in tsaro ya kashe wani mutum a filin idi. © Daily Trust
Talla

Ba tare da lokaci ba wasu matasa da suka fusata suka far wa jami’in tsaron, wanda ke aiki da hukumar  tsaron farin kaya ta Civil Defence, wanda  aka ce ya yi  harbin ne aa lokacin da ya ke ƙoƙarin cafke wani ɓata-gari.

Lamarin da auku a yayin sallar idi a Gusau, babban birnin jihar Zamfara ya fusata al’umma tare da haddasa tankiya a yankin, inda har fusatattun  matsasa suka banka wa motar Civil Defence ɗin wuta.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara, ta bakin kakakinta, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tuni aka kame jami’an da ke da hannu a lamarin.

Sai dai mai magana da yawun Hukumar Tsaron Farin kaya a a jihar Zamfara, Ikor Oche,  ya musanta zargin cewa jami’an Civil Defence ne suka yi harbi mutumin.

Oche ya ce hukumar NSCDC ta ƙaddamar da bincike don gano ainihin abin da ya  auku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.