Isa ga babban shafi

Rasuwar Saratu Gidado ta girgiza masana'antar fina finan Kannywood

Najeriya – Najeriya tayi rashin daya daga cikin jaruman masu shirin fina finan ta a bangaren Kannywood,  Saratu Gidado wadda aka fi sani da suna Daso da ta rasu yau talata a birnin Kano.

'Yar wasan fim din Hausa, Saratu Gidado Daso
'Yar wasan fim din Hausa, Saratu Gidado Daso Wikipedia
Talla

Rahotanni sun ce Gidado ta rasu ne bayan tayi sahur, inda aka samu gawar ta da safe.

An haifi marigayiyar ce a ranar 17 ga watan Janairun shekarar 1968 a birnin Kano, kuma ta rasu tana da shekaru 56.

Jarumar ta taka gagarumar rawa a shirin fina finan Kannywood tun bayan fara fitowar ta a shekara ta 2000 a shirin 'Linzami da Wuta'.

Wasu daga cikin fina finan da ta fito sun hada da Nagari da Gidauniya da Mashi da kuma Sansani.

Wasu bayanai sun ce a jiya, Jarumar ta wallafa hotan ta a shafin fezbuk tare da sanya wakar 'Daga gobe ne', inda ta dauki wani bututu kamar tana duba jinjirin watan Shawwal.

Marigayiya Saratu Gidado
Marigayiya Saratu Gidado © Daily Trust

Rasuwar Gidado ko kuma Daso ta jefa rudani a tsakanin abokan aikin ta da kuma masu sha'awar rawar da take takawa a cikin fina finan Kannywood, cikin su harda sabon shugaban Cibiyar horar da masu sana'ar fina finai ta Najeriya, Ali Nuhu.

Kafofin sada zumunta na ci gaba da yada sanarwar rasuwar ta da kuma wasu hotunna jarumar tare da mata addu'ar Allah ya mata rahama.

Makama Sani Mu'azu ya bayyana Daso a matsayin gwarzuwar da ta bada gagarumar gudumawa a wannan masana'anta, abinda ya sa ta farin jini a ciki da wajen Najeriya.

Mu'azu wanda ya taba rike mukamin shugaban masu shirin fina finan Najeriya baki daya, yace za'a dinga tuna ta a kan rawar da ta taka daban daban a fina finai da dana wajen fadakarwa da ilmantarwa tare da janyo hankalin jama'a a fina finan Hausa da na Turaci baki daya.

Makama yace sun yi aiki tare da Daso a fina finai, ciki harda shirin Dan-Gari da ya jagoranta, wadda ya bai wa Daso daman zama tare da iyalansa a garin Jos, kuma ya yaba sosai da kwarewar ta da kuma jajircewar ta.

Mu'azu ya yi amfani da wannan dama wajen aikewa da sakon ta'aziyar sa da kuma na kwamitin amintattun kungiyar MOPPAN da addu'ar rahama a gare ta.

Rahotanni sun ce a yammacin yau ake saran mata jana'iza a birnin Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.