Matasan Najeriya sun koma tafiya neman kudi zuwa Nijar
Matsalar tsadar rayuwa da koma bayan tattalin arziki, ya tilastawa dubban matasan Najeriya tsallakawa zuwa wasu kasashe makwafta ciki har da Jamhuriyar Nijar domin neman aiki ko gudanar da harkokin kasuwanci.
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:44
Al'ummar kasar dai na ci gaba da kokawa bisa matsalar tsadar rayuwa, tun bayan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur, yayin da darajar kudin kasar ya samu koma baya.
Wannan matsala ta haifar da tsadar kayayyaki, kama daga abinci zuwa sufuri, abin da ya gigita jama'a.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Rukayya Abba Kabara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu