Isa ga babban shafi
labarin aminiya

An kashe ‘yan bindiga 18 a kauyen Filato

Aƙalla ’yan bindiga 18 ne aka kashe yayin da aka ƙwato bindigogi da dama a ranar Litinin a wani samame da jami’an tsaro na DSS, da ‘yan sanda da ‘yan banga suka kai a Zurak Campani da ke Karamar Hukumar Wase a Jihar Filato. 

'Yan bindiga sun addabi wasu jihoji a arewacin Najeriya
'Yan bindiga sun addabi wasu jihoji a arewacin Najeriya © dailypost
Talla

Majiyarmu daga yankin ta bayyana cewa an kashe ‘yan bindigar ne tare da masu yi musu leken asiri da kuma wasu sarakunan gargajiya da al’ummar yankin ke ganin sun ci amanarsu.

Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne makonni biyu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a wata kasuwa da ke Zurak Campani, inda suka kashe mutane bakwai.

Wani shugaban matasa a Wase, Shafi’i Sambo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sambo ya ce an kashe masu laifin ne a wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro na DSS da ‘yan sanda da kuma ‘yan banga suka yi, inda suka bi sawun ‘yan bindigar har maɓoyarsu.

Ya bayyana cewa an kai wa ‘yan bindigar samame ne a lokacin da suke wani taro a cikin jeji.

“Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a yayin da suke gudanar da taro a yankin.

“An cimma nasarar ce bayan wani samamen haɗin gwiwa da ‘yan sanda, DSS, da ‘yan banga daga Wase da ma wasu makwabta daga Jihar Taraba suka kai,” inji shugaban matasan.

Aminiya ta yi rashin sa’a a ƙoƙarin da ta yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Filato, DSP Alabo Alfred.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.