Isa ga babban shafi

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon shugaban ƙasar Senegal

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban kasar Senegal na biyar a tarihin kasar, a wani ƙatsaitatcen biki da aka yi a wani ɗakin taro da ke wajen birni Dakar.

Bassirou Diomaye Faye yayin gabatar da jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024.
Bassirou Diomaye Faye yayin gabatar da jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024. AP - Sylvain Cherkaoui
Talla

Bassirou Diyomaye Faye, wanda kusan makonni biyu da suka gabata yana matsayin ɗan takarar adawa garƙame a gidan yari, bayan maye gurbin abokin tafiyarsa jigon adawar kasar Ousmane Sonko - shugaban jam’iyyar (Pastef) – tun a zagayen farko ya lashe zaɓen shugaban kasar na ranar 24 ga watan Maris, don haka a wannan Talata 2 ga watan Afrilu ya sha runtsuwar kama aiki a matsayin shughaban kasar na biyar kuma mafi karancin shekaru a tarihin kasarsa.

Bassirou Diomaye Faye yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024.
Bassirou Diomaye Faye yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024. AP - Sylvain Cherkaoui

Faye mai shekaru 44 sanye da bakaƙen kot, ya ɗage hannunsa na dama, a gaban daruruwan jami'an kasar Senegal da kuma shugabannin kasashen Afirka bakwai da suka hallara zauren taro da ke cibiyar baje kolin sabon garin Diamniadio, wajen Dakar babban birinin kasar.

“Ina tsaye Allah ya na gani na, a gaban al'ummar Senegal, na rantse zan sauke nauyi na aika shugaban kasar Senegal cikin gaskiya da adalci, ta hanyar kiyaye tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkinmu da Dokokin kasa."

Mista Diamaye Faye ya yi nasara da kashi 54 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaɓen da aka jinkirta a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam'iyya mai mulki.

A ranar Juma'a ne Kotun Kolin kasar ta yammacin Afirka, ta tabbatar da Mista Faye a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na ranar 24 ga watan Maris 2024.

Bassirou Diomaye Faye yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024.
Bassirou Diomaye Faye yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024. AP - Sylvain Cherkaoui

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu wanda kuma shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO ya kasance cikin shugabanni kusan 15 ko wakilansu da suka halarci bikin.

Bassirou Diomaye Faye yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024.
Bassirou Diomaye Faye yayin rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Senegal a birnin Dakar na kasar Senegal, Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024. REUTERS - Zohra Bensemra

Kafin a kai ga zaben, kasar ta yi fama da tarzoma mummuna bayan da Shugaba Sall ya yi yunkurin jinkirta zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.