Isa ga babban shafi

Kotun tsarin mulkin Senegal ta amince da nasarar Faye a zaben shugaban ƙasa

Kutun tsarin mulkin kasar Senegal ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye ya samu, a zaben shugaban kasar, lamarin da ya share hanyar rantsar da shi a matsayin shugaban kasar na biyar.

Zaɓeɓɓen shugaban kasar Senegal Basirou Faye lokacin da ya gana da shugaba mai ci Macky Sall a fadar gwamnati da ke Dakar.28/03/24
Zaɓeɓɓen shugaban kasar Senegal Basirou Faye lokacin da ya gana da shugaba mai ci Macky Sall a fadar gwamnati da ke Dakar.28/03/24 AFP - -
Talla

Kotun ta amince da sakamakon wucin gadi da aka sanar a ranar Laraba bisa la’akari da alkaluman da aka tara a rumfunan zabe, da kuma rashin kalubalantar sakamakon daga sauran ‘yan takara.

Faye ya samu sama da kashi 54% na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar, inda dan takarar jam'iyyar mai mulki Amadou Ba ya samu kashi 35%.

A ranar 2 ga watan Afrilu ne ake sa ran za a rantsar da shi domin maye gurbin shugaba Macky Sall mai barin gado.

Nasarar Faye dai ita ce ta farko da dan takarar adawar Senegal ya lashe tun a zagayen farko tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960.

A ranar Juma'a, kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta taya Faye murnar nasarar da ya samu, tare da jinjinawa yarjejeniyar amincewa da sakamako da aka cimma tsakanin ‘yan takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.