Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya za ta samar da sabbin dabarun yaki da ‘yan fashi da makami -Shettima

A Najeriya ,mataimakin shugaban kasa Kashim Shettina ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta samar da sabbin dabarun yaki da ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a sassan kasar .

Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima © kashim shettima facebook
Talla

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina a jiya Asabar.

Wani jami'in tsaro a jihar Kastina
Wani jami'in tsaro a jihar Kastina PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Wannan tabbacin ya zo ne kwana guda bayan gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya roki gwamnatin tarayya da ta kara tura mutane da kayan aiki domin tallafa wa jihar a lokutan da ta ke fama da hare-haren ‘yan fashi da makami.

Shettima ya ce gwamnatin tarayya za ta tura duk wani abu da kwararrun da ake bukata domin dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Tsohon Shugaban Najeriya Mohammadu buhari ,
Tsohon Shugaban Najeriya Mohammadu buhari , REUTERS - Afolabi Sotunde

Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu rakiyar ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki Sanata Atiku Bagudu da na noma da samar da abinci Alhaji Abubakar Kyari da kuma tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha sun kuma kai gaisuwar ban girma ga Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar a fadar sa dake Daura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.