Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe mutane, bayan sace 24, da kona kasuwa da gidaje a Katsina

Wasu ‘yan ta’adda sun kashe mazauna kauyen Gangara da ke karamar hukumar Jibia 5 tare da raunata wasu 7 a wani hari da suka kai a  daren ranar Alhamis a jihar Katsina. Maharan sun kuma yi awon gaba da mazauna yankin 24, yawancinsu mata da kananan yara.

Wata daliba da ta tsallake rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka sace dalibai a arewacin Najeriya
Wata daliba da ta tsallake rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka sace dalibai a arewacin Najeriya AP - Ibrahim Mansur
Talla

A wannan hari,’yan ta’addan sun kuma kona gidaje shida da kuma kasuwar yankin.

Hakimin unguwar Gangara, Aliyu Abubakar, ya shaida jaridar  PREMIUM TIMES a Najeriya ta wayar tarho cewa, dukkan mutanen biyar da aka kashe, mazan aure ne.

“Yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 10 na dare tare da harbin  daga Sabon Garin Gangara, inda suka kashe mutum daya.

Yankin Kankara a jihar Katsina
Yankin Kankara a jihar Katsina REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Mutanen garin sun bayyana harin na baya-baya nan a matsayin  mummuna. Mutane bakwai sun samu munanan raunuka,wandada aka kai  wasu asibitocin kashi da kwararru yayin da wasu kuma suka kasance a asibitin Koyarwa na Tarayya suna karbar kulawar likitoci.

Masarautar Katsina a Najeriya
Masarautar Katsina a Najeriya jumia

Maharan sun zabi wadanda za su yi garkuwa da su ba tare da sun bayyana dalilin ba.

Basaraken garin ya ce an binne gawarwakin wadanda suka mutu tare da taimakon ‘yan banga.

Ya ce zuwan ’yan banga ne ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.