Isa ga babban shafi

Ban taba yin hannu da shugaban wata kasa ba - Peserio

Najeriya – Mai horar da kungiyar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles, Jose Peserio yace a rayuwar sa bai taba hannu da wani shugaban kasa ba, sai wannan karo da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama shi a fadar sa da ke Abuja.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da mai horar da 'yan wasan Super Eagles Jose Peserio
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da mai horar da 'yan wasan Super Eagles Jose Peserio © Nigeria presidency
Talla

Peserio ya bayyana haka ne cikin farin ciki lokacin da Tinubu ya karrama tawagar 'yan wasan da suka taka rawar gani a gasar AFCON da aka kammala a kasar Cote d'Ivoire.

Kungiyar Super Eagles ta samu lambar azurfa saboda zuwa na 2 a gasar, bayan ta sha kashi a hannun 'yan wasan Cote d'Ivoire wadanda suka lashe gasar.

Shugaba Tinubu ya jinjinawa tawagar Super Eagles wadda ta kun shi 'yan wasan da masu horar da su, tare da basu lambar girma ta kasa da kuma gidaje kyauta a birnin Abuja.

Wannan karamawar ta yi matukar farantawa Peserio rai, wanda bai boye ta a zuciyarsa, inda ya jinjinawa gwamnatin Najeriyar da kuma shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya karbe su.

A wurin ne Peserio yace a rayuwar sa bai taba hannu da wani shugaban kasa ba, sai a wannan karon.

'Yan Najeriya da dama sun bayyana gamsuwa da rawar da kungiyar Super Eagles ta taka a gasar ta AFCON duk da rashin nasarar lashe kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.