A yanzu ne 'yan wasanmu ke bukatar karfafa gwiwa ba cin fuska ba - Ahmed Musa
Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya Ahmed Musa, ya bukaci a daina cin fuskar dan wasan tsakiya na tawaga Alex Iwobi a kafofin sada zumunta, inda ya ce kwallon kafa hadin kai take kawo wa ba cin zarafi ba.
Wallafawa ranar:
Musa ya ce rashin nasara a wasa abune mai ciwo, amma bai kamata ace a rinka ware wani dan wasa ana cin zarafinsa ba, domin a cewarsa idan an samu nasara ta kowa ce haka ma akasin hakan.
Iwobi da ke buga wasa a kungiyar Fulham, na daga cikin ‘yan wasan da ake fuskantar cin fuska a shafukan sada zumunta, bayan rashin nasarar da tawagar Super Eagles ta yi a wasan karshe na gasar AFCON.
Iwobi ya goge dukkanin hotuna da bidiyo a shafinsa na Instagram bayan faruwar wancan lamari.
Sai dai jagoran tawagar ta Super Eagles Ahmed Musa, ya ce Iwobi ya bada iya gudunmuwar da ya kamata ya bada, a matsayinsa na dan wasa kuma kamar yadda kowa ne dan wasa yayi.
Ahmed Musa ya ce mai makon yada abuwan gazawa na ‘yan wasan, kamata yayi a ci gaba da mara musu baya don karfafa musu gwiwa a wannan lokaci da suke bukatar hakan.
Tsohon dan wasan Arsenal din, ya buga wasan minti 79 a karawar da suka yi da Ivory Coast, kafin a sanyo Alhassan Yusuf ya maye gurbinsa a wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu