Rigar wasan Super Eagles ta Najeriya tayi karanci a birnin Kano
Najeriya – Masu goyan bayan kungiyar Super Eagles ta Najeriya a birnin Kano sun bayyana matukar damuwar su da yadda samfurin rigar kungiyar tayi karanci da kuma tsada a birnin gabanin karawar da za'ayi yau tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.
Wallafawa ranar:
Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriyar ta ruwaito cewar, rigar da ake sayarwa naira dubu 5 yanzu haka ta tashi zuwa naira dubu 15, kuma samun ta ya yi wahala saboda yadda ake bukatar ta.
Jaridar tace wani da ya kasa samun rigar a Kano, an shaida masa cewar ana samun ta a Kaduna amma a farashin tsakanin naira dubu 20 zuwa dubu 25.
'Yan Najeriya dake sha'awar kwallon kafa kan sanya rigar kungiyar ta kasa domin jaddada goyan bayan su a duk lokacin da kasar ke wasa.
Rahotanni sun ce sakamakon nasarorin da kungiyar ta Super Eagles ke samu a wasannin da take yi na AFCON samfurin rigar tasu tayi kasuwa sosai musamman daga 'yan siyasa da kuma masu bibiyar kwallon kafa.
Daga cikin wadanda aka gani sanye da rigar harda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da gwamnonin jihohi da ministoci da kuma shugabannin majalisun tarayya da na jihohi.
Yanzu haka tawagar gwamnatin tarayya a karkashin mataimakin shugaban kasar Shettima ta isa Abidjan tare da gwamnonin Nasarawa da Katsina domin goyan bayan 'yan wasan a karawar da za suyi an jima da Cote d'Ivoire.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu