Isa ga babban shafi

Tababa da rashin tabbas sun mamaye makomar Peserio na kungiyar Super Eagles

Najeriya – Tababa da rashin tabbas sun mamaye rashin sanin makomar mai horar da 'yan wasan kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, Jose Peserio sakamakon kawo karshen wa'adin kwantiragin sa jiya lahadi kamar yadda yarjejeniyar da suka kulla da Hukumar NFF ta tanada.

Jose-Peseiro, mai horar da 'yan wasan Najeriya na Super Eagles
Jose-Peseiro, mai horar da 'yan wasan Najeriya na Super Eagles © premium times
Talla

Yayin da wasu ke ganin ya dace a ba shi wata sabuwar kwangila saboda kokarin da kungiyar Super Eagles ta yi na zuwa wasan karshe na cin kofin AFCON, sabanin yarjejeniyar da suka yi da Hukumar NFF wadda ta ba shi umarnin kai kungiyar wasan kusa da na karshe, wasu na ganin cewar ya dace a samo wani horarwar da ya fi shi kwarewa.

Kocin Najeriya José Peseirotare da Ola Aina
Kocin Najeriya José Peseirotare da Ola Aina AP - Sunday Alamba

Shi dai Peserio har albashi aka zabtare masa bara amma yaki aje aikin horar da kungiyar ta Super Eagles kana kuma ya sa ta karbuwa a gasar AFCON saboda irin nasarorin da ta samu, a wasannin da ta buga.

Wadannan nasarori da manajan ya samu yanzu haka ya jefa shugabannin hukumar kwallon kafar Najeriya cikin rudani a kan matakin da ya dace su dauka, dangane da makomar sa.

Yayin da wasu daga cikin su ke neman ganin an samu sauyi, wasu kuma na gabatar da bukatar mutunta yarjejeniyar da suka yi da manajan, ganin ya zarce mizanin da suka gindaya masa.

Magoya bayan kungiyar Super Eagles ta Najeriya
Magoya bayan kungiyar Super Eagles ta Najeriya REUTERS - LUC GNAGO

A ranar laraba mai zuwa ake saran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi tawagar 'yan wasan na Super Eagles tare da masu horar da su, domin karrama su dangane da bajintar da suka nuna a gasar da kuma yadda suka farantawa al'ummar kasar rai a kan irin nasarorin da suka samu.

Ga alama, bayan wannan biki ne za'a ji amon da hukumar NFF za tayi dangane da makomar Peserio.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.