Isa ga babban shafi
AFCON

Ivory Coast ta lashe gasar AFCON bayan doke Najeriya da kwallo 2 da 1

Ivory Coast ta shiga sahun kasashen Kamaru da Masar wadanda ke da tarihin daukar nauyin gasar cin kofin Afrika da kuma lashe kofin a lokaci guda, bayan nasararta ta doke Najeriya da kwallaye 2 da 1 a wasan karshe na gasar cikin daren jiya Lahadi.

Tawagar 'yan wasan Ivory Coast.
Tawagar 'yan wasan Ivory Coast. © Pierre René-Worms/RFI
Talla

Wannan ne karo na 3 da Ivory Coast ke lashe kofin wannan gasa a tarihi bayan nasararta a 1993 da 2015 wadanda dukkaninsu ta kai labari ta hanyar nasara a bugun fenariti.

A bangare guda, Najeriya mai tarihin lashe kofin AFCON sau 3 wannan ne karo na 8 da ta ke haskawa a wasan karshe na gasar kuma karo na 5 da ta ke shan kaye.

Tawagar Elephants ta Ivory Coast ta matukar bayar da mamaki yadda ta mamaye karawar ta jiya duk da cewa Najeriyar ta zura kwallon farko tun a minti na 38 ta hannun kyaftin dinta Williams Troost Ekong amma kuma mintuna kalilan mai masaukin bakin ta farke.

Najeriyar dai ta gaza farke kwallayen biyu har zuwa busa usur din karshe wanda kai tsaye ya baiwa Ivory Coast mai masaukin baki nasara.

Kafin yanzu dai an yi wa Najeriyar tsammanin nasarar lashe karawar lura da yadda ta lallasa Ivory Coast a haduwarsu ta farko yayin wasannin rukuni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.