Isa ga babban shafi

Tinubu ya bai wa 'yan wasan Najeriya gidaje da filaye a Abuja

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa 'yan wasan Super Eagles kyautar gidaje da filaye a babban birnin tarayya a Abuja sakamakon bajintar da suka nuna a gasar cin kofin Afrika da aka kammala a Ivory Coast, inda suka zo matsayi na biyu bayan mai masaukin baki ta doke su da ci 2-1.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da 'yan wasan Super Eagles a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da 'yan wasan Super Eagles a Abuja © Super Eagles
Talla

Shugaba Tinubu wanda ya karbi 'yan wasan na Super Eagles a wannan Talatar, ya yaba da kokarin 'yan wasan, yayin da kuma ya karrama su da lambar yabo ta kasa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan kasar ke ci gaba da sukar 'yan wasan na Super Eagles da suka ce sun yi sakaci sosai a yayin buga wasan na karshe, inda suka bari Ivory Coast ta farke kwallon da suka fara zura mata, sannan ta kara musu kwallo ta biyu ana gab da tashi wasan a ranar Lahadin da ta gabata.

Wasu daga cikin masharhanta sun ce, wasan na Super Eagles sun raina takwarorinsu na Ivory Coast ne ganin yadda suke doke su a matakin rukuni, abin da ya yaudare su har suka gaza tabuka abin kirki a wasan na karshe.

Babu shakka da dama daga cikin 'yan Najeriya sun sakankance cewa, mawuyaci ne Najeriyar ba ta sake daukar kofin ba a bana, amma  lamarin ya sauya.

Masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya sun yi ta yi wa 'yan wasan na Super Eagles ba'a tare da cin mutunci saboda gaza kawo kofin na Afrika gida.

Yanzu dai ko babu komai, 'yan wasan sun samu tukuici daga shugaban kasa da ya gwangwaje su da filaye da gidaje da kuma lambar yabo ta kasa.

Ko a lokacin da suka tsallaka matakin wasan karshe bayan sun doke Afrika ta Kudu, sai da gwamnonin APC suka yi wa 'yan wasan na Super Eagles kyautar naira miliyan 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.