Isa ga babban shafi

Matan gwamnonin Najeriya sun bukaci kafa dokar ta baci a kan miyagun kwayoyi

Najeriya – Ganin yadda ake samun karuwar matasan dake rungumar mu'amala da miyagun kwayoyi, matan gwamnonin Najeriya sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mazajen su da su kafa dokar ta baci domin dakile illar da kwayoyi ke yi a tsakanin al'umma.

Janar Muhammadu Buba Marwa - Shugaban Hukumar NDLEA
Janar Muhammadu Buba Marwa - Shugaban Hukumar NDLEA © NDLEA
Talla

Matan sun ce dokar ta bacin zata bada damar samar da kudaden da ake bukata domin tinkarar wannan matsala dake zama babbar barazana ga makomar matasan kasar.

Sanarwar da kakakin hukumar NDLEA Femi Babafemi ya gabatar tace, matan gwamnonin a karkashin jagorancin, Ambasada Olufolake Abdurazaq, matar gwamnan Kwara sun bukaci matakin ne bayan wani taron kwanaki 2 da suka yi da shugabannin hukumar NDLEA a kan illar da kwayoyin ke yi a fadin Najeriya.

Wives of Nigerian governors seeking collaboration on how to stem drug abuse
Wives of Nigerian governors seeking collaboration on how to stem drug abuse © NDLEA

Matan gwamnonin sun kuma bukaci inganta wuraren da aka tanada a jihohi domin kula da matsana da suka samu kan su a cikin halin amfani da kwayoyin dan ganin an dawo da su hanya.

Taron matan ya kuma bukaci sake duba matakan da ake dauka wajen yin tarbiya a tsakanin iyalai, wadanda suka ce ya yi rauni, inda suka bukaci iyaye su tashi tsaye wajen sauke nauyin dake kan su.

Matan sun yi alkawarin aiki tare da jami'an hukumar NDLEA da kuma sauran hukumomin tsaro wajen inganta hadin kan da ake bukata domin yaki da mu'amala da kwayoyin, yayin da kuma suka yi alkawarin bada gudumawa wajen samar da akalla cibiyoyi guda 3 da za'a dinga taimakawa irin matasan da suka shiga irin wannan mummunar dabi'ar a kowacce mazabar 'yan majalisun dattawa na jihohi.

Matan sun yaba da irin matakan da shugaban hukumar NDLEA Janar Muhammadu Buba Marwa ke dauka na kara kaimin aikin jami'an sa na dakile safara da kuma shan kwayar a cikin kasa.

A karshe Janar Marwa ya yabawa matan gwamnonin saboda sha'awar da suka nuna na aiki tare da hukumarsa domin magance wannan matsala da kuma yadda suka jure halartar taron na kwanaki 2 lura da irin ayyukan dake gaban su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.