Isa ga babban shafi

Za'a samu karuwar wadanda zasu kamu da ciwon kansa nan da 2050-WHO

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta yi hasashen cewa za’a samu karuwar mutanen da zasu kamu ciwon kansa da kaso 77 cikin 100 na da shekarar 2050, adadin da ya zarta na 2022 shekarar da ta shiga tarihin samun mafi yawan mutanen da ke kamuwa da cutar.

Kansar zata fi kamari a 'yan shekaru 40 zuwa sama
Kansar zata fi kamari a 'yan shekaru 40 zuwa sama © unsplash_ Angiola Harry
Talla

Wata hukuma da ke bincike kan yaduwar da kuma samuwar na’ukan cutar kansa, karkashin hukumar Lafiya ta duniya ce ta gudanar da wannan bincike, inda tace karuwar cutar kansar zata kasance ne saboda dalilan shan taba sigari, bulbular barasa da kuma karuwa masu ajiye teba ba gaira ba dalili.

 

Hukumar ta ce nan da shekarar 2050, yawan mutanen da zasu yi fama da cutar ta kansa zai kai miliyan 35 a fadin duniya, abinda ya zarta miliyan 20 da aka gani a 2022.

 

Binciken ya kuma ce sauyin yanayi da yanayin abincin da mutanen ke ci zai tasiri matuka wajen karuwar kansar, don haka akwai bukatar mahukunta su sake zage dantse wajen magance sauyin yanayi da gurbatar muhalli.

 

Rahoton binciken ya sanya manyan kasashen da ke gaba wajen ci gaba a matsayin kasashen da zasu zama matattarar masu ciwon na kansa, inda za’a samu karin kaso 4.8, idan aka kwatanta da 2022.

 

Sai dai kuma wannan ba yana nufin kasashe masu matsakaicin ci gaba, ko kuma ‘yan Allah baku mu samu ba sa cikin hadari ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.