Isa ga babban shafi

Zimbabwe ta fara gangamin rigakafin kwalara bayan cutar ta kashe mutane 452

Zimbabwe ta kadamar da gangamin rigakafin cutar cholera ko kuma amai da gudawa wanda ke da nufin yiwa mutum fiye da miliyan 2  rigakafin a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar wadda ta kasha daruruwan mutane tun bayan barkewarta a bara.

Dakin kula da masu cutar kwalara a Zimbabwe.
Dakin kula da masu cutar kwalara a Zimbabwe. © Namukolo Siyumbwa / Reuters
Talla

Alkaluman ma’aikatar lafiya ta Zimbabwe na nuna yadda annobar cutar ta cholera ta kashe mutane 452 cikin mutum dubu 20 da 446 da suka harbu da ita daga watan Fabarirun bara zuwa bana.

Ma’aikatar lafiyar ta bayyana cewa galibin masu harbuwa da cutar ta cholera kananan yara, wannan dalili ya tilasta daukar matakin rigakafin don basu kariya.

Zimbabwe za ta karbi alluran rigakafin cholera miliyan 2 da dubu 300 daga asusun UNICEF da hukumar lafiya ta WHO alluran da kasar za ta rarraba zuwa yankuna 29 da cutar tafi tsananta.

A cewar ma’aikatar lafiyar tuni allurai dubu 892 suka isa gareta kuma su ne ta fara gangamin rigakafinsu tun a jiya Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.