Isa ga babban shafi

Barazanar harin 'yan bindiga ta tilasta mutanen kauyukan Zamfara 10 tserewa

 Al’ummomin kauyuka 10 a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara sun tsere daga matsugunan saboda fargabar yiwuwar kai musu hari bayan barazanar da wani jagoran ‘yan bindiga na yankin Dan Nagala ya aike musu.

'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a kauyka da dama na jihar Zamfara.
'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a kauyka da dama na jihar Zamfara. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Rahotanni sun ce kauyukan da zuwa yanzu mutanensa suka tsere daga matsugunansu sun hada daGidan Soro da Maje da Fanda Hakki baya ga Hayin Dankaro da kuma Doka da Dan Gamji sai Galmuwar Hannu da Dan Katsina sannan Dakwalge da kuma Gidan Arne.

Gargadin ‘yan bindigar ga al’ummomin kauyukan 10 na zuwa ne bayan luguden wutar da sojojin Najeriya da ke karkashin Operation Hadarin Daji suka yi musu a maboyarsu da ke cikin dajin Danbassa-Buzaya.

 Yayin sumamen dakarun Sojin Najeriyar, sun gano shanu da ‘yan bindigar karkashin jagorancin Dan Nagala suka sace daga hannun daidaikun jama’a.

Wani mazaunin kauyen Gidan Soro ya shaidawa jaridar Najeriya ta Daily Trust cewa tun bayan da sojojin Najeriya suka kai sumame dajin tare da kwashe shanun dan bindigar ne makwanni 3 da suka gabata ne Dan Nagala ya aike da sakon gargadin cewa sai ya kai hari ilahirin kauyukan da ke kewaye da dajin.

A cewar rahotanni wannan dalili ya sanya al’ummomin kauyukan tserewa don kare rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.