Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun bada wa'adin kwana 7 don ceton daliban jami'ar Zamfara

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban jami’ar Gusau a jihar Zamfara a Najeriya sun bayar da wa’adin kwanaki 7 don cetar ‘yan matan ko kuma su kashe su, matukar ba a cika bukatun da suka mikawa gwamnatin kasar ba.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Cikin wani sakon gargadi da ‘yan bindigar suka aikewa iyayen ‘yan matan sun yi barazanar kashe su matukar gwamnati ba ta biya musu dukkanin bukatu da sharuddan da suka gindaya gabanin sakin daliban ba.

Guda cikin iyayen daliban da ya bayyana aike masa sakon barazanar kisan daliban tun a Larabar da ta gabata, ya roki gwamnati ta tattauna da ‘yan bindigar don ceto rayuwar yaran kwatankwacin tattaunawar da ta yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Iyayen daliban da dama wadanda jaridar Daily Trust ta zanta da su, sun tabbatar da samun sakon watsap da ke barazanar kisan ‘ya’yan nasu nan da kwanaki 7 masu zuwa matukar ba a yi abin da ‘yan bindigar ke so ba.

Tun bayan sace daliban da ‘yan bindigar suka yi, rahotanni sun ce ofishin babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da shalkwatar tsaron Najeriyar dama hukumar tsaron farin kaya ta DSS na tattaunawar sirri da ‘yan bindigar don kubutar da daliban.

A ranar 21 ga watan Satumbar da ya gabata ne, guda cikin jagororin ‘yan bindigar Ali Kachalla ya jagoranci sace ‘yan matan daliban jami’ar Gusau da ke jihar ta Zamfara su akalla 50.

Wasu hare-haren Sojin Najeriya a ranar 11 ga watan Disamban nan sun yi ikirarin kisan Kachalla batun da shalkwatar tsaron kasar ta tabbatar a ranae 16 ga watan.

Baya ga Kachalla harin sojojin ta sama a dajin karamar hukumar Munya ta jihar Neja ya kuma kashe tarin 'yan bindigar galibinsu masu hannu a satar Daliban.

Sai dai wasu bayanai na nuna cewa ‘yan bindigar sun yi zaben sabon shugaba wanda a yanzu shi ke da ta cewa game da yiwuwar sakin yaran ko akasin haka, wanda kuma karon farko ya aike da wannan barazana duk da yadda mahukunta suka shafe tsawon makwanni suna kokarin ceto rayukan daliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.