Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun halaka 'yan ta'adda fiye da 100 a Zamfara

Bayanai daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce, sojojin kasar sun samu nasarar halaka ‘yan ta’adda sama da 100 a yankin karamar hukumar Maru.

Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya.
Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya. © Daily Trust
Talla

Wasu  majiyoyi sun ce ‘yan bindigar masu yawan gaske sun gamo da gamonsu ne a lokacin da suke kokarin tsallaka wa cikin Kebbi da nufin kaddamar da hare-hare kan kauyukan da suke yankin jihar.

Har ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan adadin ‘yan ta’addan da dakarun Najeriyar suka halaka, sai dai wani mazauni yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida mana cewa suna kyautata zaton adadin 'yan bindigar da aka kashe ya zarce yadda ake tunani.

Majiyar ta ce jirgin yakin sojin Najeriyar ya yi wa 'yan ta'addan ruwann wuta a yankuna da dama da ke iyakar Zamfara da jihar Neja, yayin da suka yi yunkurin tserewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.