Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Ruwan Doruwa da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka kashe dan sanda tare da garkuwa da mutane 13. 

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust
Talla

Mazauna yankin sun ce 'yan ta'addar sun sace mutane 13 da suka kunshi mata shida da maza biyar da kuma kananan yara biyu yayin harin na jiya Lahadi da suka dauki sama da sa'o'i biyu. 

A cewar wani shugaban al’ummar yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ’Yan ta’addan sun isa kauyen ne da misalin daya na dare, inda suka yi wa kauyen kawanya tare da harbi kan mai uwa da wabi. 

Jami’in ya ce akasarin matan da aka yi garkuwa da su matan aure ne. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.