Isa ga babban shafi

Wasu al'ummomin Zamfara za su biya tarar miliyoyi ga dan ta'adda saboda sun fallasa shi

‘Yan bindiga sun ci tarar wasu al’ummomi 3 a karamar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara saboda zarginsu da kai wa jami’an tsaro bayanai a kansu.

Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga
Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga © Channels
Talla

Al’ummomin za su biya naira miliyan 3 kowanne ga wani kasurgumin dan bindiga da aka fi sani da Dan Bokolo don kauce wa hare -hare.

Dan ta’addan dai ya fusata ne da yadda al’ummomin Kamarawa, Sabuwar Kamarawa da Gebe suka yi ta kwalmata bayanai a kansa ga jami’an tsaro.

Rahotanni daga yankunan da abin ya  shafa dai  sun ce wannan matsalar ta baya bayan nan ta tashi ne bayan da jami’an tsaron Najeriya suka kama wani dan uwan uwan kasurgumin dan ta’adda mai suna Abdullahi a yayin da ya je sayayya kasuwa, kuma an zargi al’ummar yankin ne da tsegunta wa jami’an inda ya ke.

Biyan wannan tara don samun kariya ya saba wa matsayin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, wanda ya jaddada cewa ba zai yi sulhu da ‘yan ta’adda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.