Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da masu bautar kasa a Najeriya

Bayanai daga jihar Zamfara ta Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan bautar kasa 8, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Sokoto inda aka tura su don yin aikin bautar kasa.

Wasu masu aikin hidimar kasa a Najeriya.
Wasu masu aikin hidimar kasa a Najeriya. © rfi
Talla

Tun farko daliban su 11 sun shiga motar haya mallakin gwamnatin jihar Akwa Ibom da nufin zuwa jihar Sokoto, inda aka tura su don aikin bautar-kasar, sai dai fitar su daga birnin Gusau ke da wuya 'yan bindigar suka far musu.

Rahotanni sun nuna cewa uku daga cikinsu sun yi nasarar tserewa, sai dai ‘yan bindigar sun shiga da guda 8 da kuma direban motar cikin daji.

Wani jami’i daga kamfanin motocin hayar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba zato ba tsammani suka ga ‘yan bindigar a tsakiyar titi, abin da ya tilasta wa direban motar taka burki, nan take kuma suka bukaci su fito daga motar sannan suka kada daliban da direban motar cikin daji, bayan da saura suka tsere.

Guda daga cikin iyalan daliban ya shaida wa manema labarai cewa tuni ‘yan bindigar suka tuntube su tare da bukatar su kai naira miliyan 4 kan kowanne dalibi a matsayin kudin fansa.

RFI Hausa ta yi iya bakin kokarinta wajen jin ta bakin jami’an tsaro da bangaren gwamnatin jihar Zamfara don neman karin bayani, amma hakan ya ci-tura, inda kakakin 'yan sandan jihar Yazid Abubakar ya gaza bayar da  bayani duk da kiran da muka rika yi masa da kuma alkwarin ba mu cikakken bayani.

Shi kuma mataimakin gwamna kan harkokin yada labarai Mustapha Jafaru Kaura bai dauki waya ba bayan mun kira shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.