Isa ga babban shafi

Buhari bai taba sanya baki a Mulki na ba – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce tun bayan rantsar da shi kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun bara, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba sanya baki a jagorancin kasar da yake gudanarwa ba. 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, tare da tsohon shugaba Muhammad Buhari.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, tare da tsohon shugaba Muhammad Buhari. © BashirAhmad
Talla

Tinubu ya kuma kara da cewar, tsohon shugaban bai gabatar da ko da mutum guda ba domin nada shi a wani mukami a karkashin sabuwar gwamnatin da kasar ta samu bayan zaben da ya gudana a watan Fabarairun bara ba. 

Yayin da yake gabatar da jawabi wajen kaddamar da littafin da tsohon mai bai wa Buhari shawara a harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rubuta, a kan yadda Buharin ya gudanar da mulkinsa, shugaba Tinubu ya ce Buhari ya cika alkawarin da ya daukarwa kansa cewar zai zauna nesa da birnin Abuja, kuma ba zai sanya baki a cikin mulkin da ke gudana ba. 

Shugaban ya jinjina wa Buhari a kan hadin kan da suka kulla wajen ciyar da dimokiradiyar Najeriya gaba, yayin da ya sake jaddada rashin katsalandar din tsohon janar na sojin a mulkinsa. 

Tinubu ya ce in banda kiran da yake yi wa Buhari ta waya domin sanin halin da yake ciki da kuma gonarsa, babu wata tintibar da ke gudana, ko kuma kamun kafa domin nada wani a mukamin gwamnati daga tsohon shugaban.

Shugaban ya yi wa Buhari shagube daga karshe cewar, sun rufe iyakar Jamhuriyar Nijar domin hana shi barin kasar kamar yadda ya ce za a dame shi bayan sauka daga karagar mulki.

Cikin wadanda suka halarci bikin kaddamar da littafin har da tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ministocin da suka yi aiki tare da Buhari. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.