Isa ga babban shafi

Buhari ya kama hanyar zuwa Daura bayan mika mulki ga Tinubu

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanyar komawa mahaifarsa a garin Daura da ke jihar Katsina, bayan da ya mika mulki ga sabon shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria Presidency
Talla

Bikin rantsar da sabon shugaban Najeriyar da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya gudana ne a babban filin taro na Eagle Square da ke birnin Abuja a wannan litinin.

Gabanin mika ragamar shugabancin Najeriya ga Tinubu, Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi iyaka kokarinta wajen kyautata al’amura a kasar, kuma yana da kwarin gwiwar cewa Najeriyar da zai mika wa sabon shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu cigaba fiye da halin da take ciki a shekarar 2015.

Tsohon shugaban, wanda ya bayyana hake cikin wani jawabi da ya gabatar da aka watsa da kafofin talabijin a ranar Lahadi, ya kuma nemi afuwar ‘yan Najeriya kan wasu daga cikin matakan gwamnatinsa da suka haifar da matsi.

Tun a lokacin da ya rage watanni wa’adin tsohon shugaban Najeriyar yak are, yake nanata cewar ya matsu ya koma gida domin samun damar hutu, daga dimbin kalubalen shugabancin da ya fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.