Isa ga babban shafi

Tinubu ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin zababben shugaban Najeriya na 7

Yau litinin zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya yi nasarar lashe zaben watan Fabarairu, ya yi rantsuwar kama aiki, bayan mika masa mulkin da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi, yayin bikin da ya gudana a dandalin Eagle Square da ke Abuja fadar gwamnatin kasar. 

Bola Ahmed Tinubu tare da Muhammadu Buhari a wurin bikin karrama zababben shugaban kasar a Abuja.
Bola Ahmed Tinubu tare da Muhammadu Buhari a wurin bikin karrama zababben shugaban kasar a Abuja. © Nigeria Presidency
Talla

An dai rantsar da zababben shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne duk kuwa da cewa jam’iyyun ‘yan adawa sun yi tsayuwar gwamen jaki wajen ganin an saurari korafin da suka kai gaban kotun sauraron kararrakin zabe. 

Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda  ya doke abokan hamayyarsa na PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP. 

A yayin da wasu ‘yan Najeriya suka shirya kayayyakin kade –kade da bushe –bushe don bikin tarbar sabuwar gwamnati a wannan rana mai mahimmanci a tarihin kasar, wasu da suke zargin jam’iyya  mai mulki da hukumar zaben kasar da yin abin da suka kira dauki dora, zuba ido suka yi don ganin yadda za ta kaya a game da korafe-korafen da aka shigar gaban kotun sauraron kararrakin zabe. 

Bola Ahmed Tinubu dai na matsayin zababben shugaba na 7 da Najeriya ta gani karkashin mulkin demokradiyya, kuma shugabannin da suka gabace shi sun kunshi, Nnamdi Azikiwe 1963 zuwa 1966 sannan Shehu Shagari 1979 zuwa 1983 kana Olusegun Obasanjo 1999 zuwa 2007 tukuna Umaru Musa 'Yar Adua 2007 zuwa 2009.

Sauran sun kunshi Goodluck Ebele Jonathan 2009 zuwa 2015 kana shugaba Muhammadu Buhari 2015 zuwa 2023 yayinda Tinubu ke shirin karbar ragamar Najeriyar a yau litinin 29 ga watan Mayu.

Rahotanni daga Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya na cewa manyan baki da suka hada da shugabannin wasu kasashen nahiyar Afrika kamar Jamhuriya Nijar, Rwanda da Tanzania sun isa birnin tun a jiya Lahadi, gabanin bikin rantsarwar na yau litinin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.