AFDB ya bukaci Tinubu ya rage kudin da ake kashe wa tafiyar da mulkin Najeriya
Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adeshina, ya bukaci zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da ya rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da mulki.
Wallafawa ranar:
Adeshina wanda tsohon ministan Najeriya ne ya bayyana haka yayin taron bita da kwamitin mika mulki ta shirya gabanin rantsar da Bola Tinubu ranar Litinin a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.
Adesina ya ce makuden kudade da ake kashewa a bangaren gudanar da gwamnati ya ninka wanda ake kashewa wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasa, kuma hakan na mummunan tasirin wajen hana ci gaban Najeriya a cewarsa.
Ba'a kashe kudin da ya kamata wajen raya kasa
Wani rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Najeriya a matsayi na 167 cikin kasashe 174 da ke ware kudi da bai taka kara ya karya ba a fannin ayyukan ci gaba.
Ya roki Tinubu da ya tashi tsaye wajen kalubalantar mulki tun a ranar farko da zai karbi ragamar jagorancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu