Isa ga babban shafi

Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaben Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar lashe zaben shugabancin kasar da yayi, bayan karawa da ‘yan takara 17 daga jam’iyyu daban daban. 

Shugaba Najeriya mai barin gado Muhammadu Buhari tare da shugaba mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu.
Shugaba Najeriya mai barin gado Muhammadu Buhari tare da shugaba mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu. NAN
Talla

Mai Magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba ya ruwaito shugaban na cewa mutane ne suka zabi Tinubu saboda cancantarsa ta iya jagorantar Najeriya yana mai cewa yanzu haka zai fara aiki tare da shi don shirye-shiryen mika mulki.

Shugaban ya bayyana zaben Najeriya a matsayin, mafi girma a Afirka, inda yayi fatan ya kasance abin misali a yankin yammacin Afirka da ya fuskanci koma-baya da juyin mulkin soja a shekarun baya-bayan nan. 

A cewar Buhari, yadda zaben na bana ya guda manuniya ce kan karfafuwar demokradiyyar a kasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika, lura da yadda jihohi da dama suka sauya matsaya daga jam’iyyun da suke mulkinsu zuwa was una daban kamar jihar Katsina wadda ta zabi PDP da kuma Lagos mahaifar zababben shugaban da ta zabi Bola Tinubu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.