Isa ga babban shafi

Takaitaccen tarihin zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ya lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye bayan samun fiye da kashi 25 na yawan kuri’un da aka kada a jihohi 30 cikin 36, fitaccen dan siyasa ne da ya rike mukamin gwamna na wa’adi 2 haka zalika Sanata a jamhuriyya ta 3.

Bola Tinubu zababben shugaban Najeriya.
Bola Tinubu zababben shugaban Najeriya. REUTERS - JAMES OATWAY
Talla

An haifi Bola Ahmed Adekunle Tinubu a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952 a jihar Lagos da ke kudanccin Najeriya, inda ya yi makarantar firamare a ta St. John da ke Aroloya a Lagos kafin daga bisani ya ci gaba da karantunsa a matakin farko-farko a garin Ibadan.

Tinubu ya yi balaguro zuwa Amurka a 1975 domin karatun digiri a fannin Akanta a Kwalajin Richard J. Daley da ke Chicago.

Bayan kammala karatunsa, Tinubu ya yi aiki a wurare daban-daban da suka hada da kamfanin mai na Mobil a matsayin akanta kafin ya koma fagen siyasa a 1992 karkashain jam’iyyar Social Democratic Party, inda ya lashe kujerar sanata.

Sai dai a shekarar 1993, wato bayan tsohon shugaban kasar marigayi Janar Sani Abacha ya rusa majalisar dattawan Najeriya, Tinubu ya zama dan rajin neman tabbatar da demokradiyya a kasar, yayin da a 1994, aka tilasta masa ficewa daga kasar.

Ya koma Najeriya ne a 1998 bayan rasuwar shugaba Abacha, inda daga nan kuma ya sake matsa kaimi a fagen gwagwarmayar siyasa.

Tinubu wanda shi ne ma’assasin jam’iyyar ACN ya zama gwamnan jihar Lagos bayan zaben da aka yi a 1999, yayin da ya yi tazarce har zuwa shekarar 2007 daga wancan lokaci ne kuma y afara harin mukamin shugaban kasa.

Tinubu wanda ya jima yana neman shugabancin Najeriya, a lokuta da dama ya sadaukar da takarar shi ga wasu tsiraru musamman bayan hadakar da ta samar da jam’iyyar APC a shekarar 2014 wadda ta kai ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari a 2015 da 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.