Isa ga babban shafi
TARON SAUYIN YANAYI

Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila a kan matsalar sauyin yanayi

Najeriya – Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila a Dubai, inda shugabannin biyu ke halartar taron sauyin yanayi na Majalisar dinkin duniya da aka bude yau.

Sarki Charles na Ingila da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Sarki Charles na Ingila da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © Daily Trust
Talla

Yayin da yake tsokaci bayan ganawar wadda aka yi a sirrance, Tinubu yace sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya rabawa manema labarai tace, taron wani yunkuri ne na bunkasa dangantaka da kuma aiki tare tsakanin Najeriya da Birtaniya, yayin da aka bayyana fatar ganin an samu gagarumar ci gaba da ta fannin shatawa duniya matakan inganta muhalli a taron COP 28.

Lokacin ganawar Sarki Charles da shugaba Bola Tinubu a Dubai
Lokacin ganawar Sarki Charles da shugaba Bola Tinubu a Dubai © Daily Trust

Kakakin shugaban yace Tinubu zai yi amfani da wannan taro wajen gabatar da bukatar samar da karin kudade da kuma taimako ga kasashe masu tasowa wajen rage radadin matsalar sauyin yanayin da suke fuskanta.

Birtaniya ce ta yiwa Najeriya mulkin mallaka, kuma har yanzu kasashen na ci gaba da aiki tare a karkashin kasashe renon Ingila da ake kira 'Commonwealth'.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.