Isa ga babban shafi
KANNYWOOD

Jaruman Kannywood na alhinin mutuwar Aminu S. Bono

Allah ya yiwa fitaccen darakta kuma jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, wato Aminu S Bono rasuwa.

Marigayi Aminu S. Bono kenan
Marigayi Aminu S. Bono kenan © Bono/Instagram
Talla

Jarumin ya rasu ne, bayan fama da ciwon kai na gajeren lokaci. Kuma ya rasu ya bar mace guda da kuma yara uku.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El- Mustapha ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na instagram.

Jaruman Kannywood na ci gaba da jimamin mutuwar jarumin da tazo musu a ba zata, inda da dama daga cikinsu ke bayyana yadda suka rabu da shi, kafin daga bisani cikin sa'o'i kalilan da tafiyar sa gida,suka samu labarin mutuwarsa da yammacin ranar Litinin, wato 20 ga watan Nuwamba, 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.