Isa ga babban shafi
ZABEN GWAMNA

Kotun daukaka kara ta soke zaben gwamnan Filato na PDP, ta mikawa APC

Najeriya – Kotun daukaka kara a Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, yayin da ta bayyana Nentawe Goshwe a matsayin zababben gwamna, sakamakon abinda ta kira rashin bin umarnin kotu da jam'iyyar PDP tayi wajen tsayar da 'dan takara.

Farfajiyar wata kotu a Najeriya.
Farfajiyar wata kotu a Najeriya. Naij.com
Talla

Alkalan kotun guda 3 a karkashin jagorancin Williams-Dawodu suka bayyana hukuncin ba tare da wata hamayya ba a tsakaninsu, inda suka ce matakan da jam’iyyar PDP ta dauka wajen tsayar da ‘dan takara ya sabawa sashe na 285, sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Nentawe Goshwe da kotu ta bada umarnin mika masa takardar shaidar nasara zabe
Nentawe Goshwe da kotu ta bada umarnin mika masa takardar shaidar nasara zabe © Nentawe facebook

Alkalan sun ce Nentawe Goshwe na Jam’iyyar APC ya samu nasarar shari’a ce saboda korafin da ya gabatar ana iya gabatar da ita gabanin zabe da kuma bayan zabe a karkashin sashe na 177 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da kuma sashe 80 da 82 na kundin zaben shekarar 2022.

Alkalan sun ce sun amince da matsayin mai gabatar da kara Goshwe cewar PDP taki mutunta umarnin babban kotun jihar Filato, a karar da Bitrus Kaze da wasu mutane 11 suka shigar a kan jam’iyyar PDP da wasu mutane 24 na bukatar sake zaben cikin gida na samun shugabannin jam’iyyar PDP da kuma umarnin kotun daukaka kara mai lamba CA/J1/93/2021, wanda hakan ya zama taka doka.

Saboda wadannan dalilai, alkalan kotun daukaka karar guda 3 sun jingine hukuncin da kotun zabe ta gabatar wanda suka ce ya sabawa bukatar yin adalci wajen kin amincewa da karar Goshwe.

Sakamakon haka, alkalan kotun sun umarci hukumar zabe da ta janye takardar shaidar nasarar zaben da ta baiwa Muftwang domin gabatar da wani sabo ga Goshwe a matsayin zababben gwamnan jihar Filato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.