Isa ga babban shafi
Zaben gwamnan Kano

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da korar Abba Kabir a matsayin gwmanan Kano

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja babban birnin Najeriya ta kori gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, tare da tabbatar da Dakta Yusuf Nasiru Gawuna amatsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf © Abba Kabir Yusuf
Talla

Kotun mai alkalai uku ta amince da hukucin kotun sauraren kararrakin zabe karkashin mai shara’a Oluyemi Akintan Osadebay da ta kori Abba Gida-Gida a ranar 20 ga watan Satumba a matsayin ta yi daidai.

Kotun dai ta soke kuri’un Abba Yusuf dubu dari da 65 da dari 663, inda ta kafa hujja da cewa babu sahannun hukumar zaben kasar INEC a jikinsu.

Abba ya lashe zaben gwaman Kano

A ranar 18 ga watan Maris din wannan shekarar ne hukumar INEC ta sanar da gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jahar, bayan da ya samu kuri’u miliyan daya da dubu 19 da dari 602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu kuri’u dubu dari 890 da dari 705.

Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe a amatsayin babu adalci tare da rugawa zuwa kotun daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.