Isa ga babban shafi

Najeriya: Kallo ya koma sama tsakanin Gawuna da Abba Gida-Gida a Kano

A wannan Jumma'a 17 ga wata Nuwambar 2023 kotun daukaka kara ta sanya a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka, inda yake kalubalantar soke nasarar zabensa.

Hotun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma abokin karawarsa a kotu Dr Nasiru Gawuna.
Hotun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma abokin karawarsa a kotu Dr Nasiru Gawuna. © RFI/HAUSA
Talla

Abba Gida-Gida ya garzaya gaban kotun daukaka kara, bayan da kotun korafe-korafen zabe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta soke nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam'iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna tsohon mataimakin gwamnan jihar ne halastaccen wanda ya yi nasara a zaben.

Kotun dai ta soke kuri’un Abba Yusuf dubu dari da 65 da dari 663, inda ta kafa hujja da cewa babu sahannun hukumar zaben kasar INEC a jikinsu.

A ranar 18 ga watan Maris din wannan shekarar ne hukumar INEC ta sanar da gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jahar, bayan da ya samu kuri’u miliyan daya da dubu 19 da dari 602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu kuri’u dubu dari 890 da dari 705.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.