Hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da mutane sama da 100 a jihar Taraba
Hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da mutane sama da 100 a kamar hukumar Ardo Kola na jihar Taraba da ke shiyar arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Talla
Fasinjojin da ke cikin jirgin ruwan da ya kife da dama ne aka ruwaito cewar sun bace, wadanda masu linkaya ke ci gaba da laluben ko za samu nasarar ceto su.
Wakilinmu Ahmad Alhassan ya ce jami’an na ceto sun samu nasarar tsamo gawarwakin mutane 15 kamar yadda za a ji cikin rahoton da ya aiko mana.
Rahoto kan kifewar jirgin ruwa dauke da mutane sama da 100 a Taraba
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu