Rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ ta ceto daliban jami’ar tarayya na Gusau
A Najeriya ,sojojin da ke aiki da rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun ceto daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara, bayan sun yi artabu da ‘yan ta’adda da safiyar yau Lahadi.
Wallafawa ranar:
Rahotanni na nuni cewa an yi garkuwa da daliban ne a ranar Asabar a lokacin da ‘yan ta’addan suka kai farmaki a wasu gidajen kwanan dalibai da ke Sabon Garin Damba, Gusau, inda suka tafi da dalibai hudu.
Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan ta'addan za su kai hari a dakunan kwanan dalibai na jami'ar cikin kasa da kwanaki 30. Kakakin rundunar sojojin Najeriya ta Birged 1 da ke Gusau, Ibrahim Yahaya, ya ce yayin da biyu daga cikin daliban suka tsere a yayin musayar wuta tsakanin sojojin da 'yan ta'addar, sojojin sun ceto sauran daliban biyun da ke hannun yan ta’adda yayin arangamar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu