‘Yan bindiga sun kutsa kai jami’ar Gusau inda suka yi garkuwa da dalibai da malamai
Bayanai daga jihar Zamfara a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kutsa kai jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau inda suka yi garkuwa da dalibai da malamai da dama. ‘Yan bindigar masu matukar yawa sun kewaye unguwar sabon gida dake karamar hukumar Bungudu, kafin daga bisani su kutsa kai cikin jami’ar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun hari dakunan kwanan dalibai guda uku, kuma sun kwashe dukannin daliban da ke cikin su.
Duk da cewa jami’an sojoji sun mayar da martani kan harin amma duk da haka ‘yan bindigar sun yi nasarar tafiya da daliban har ma da wasu daga cikin malaman su.
An gano cewa ‘yan bindigar sun raba kan su biyu, inda wasu suka tafi da dalibai, wasu kuma suka tsaya suka tunkari sojoji.
Wasu ganau sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun mamaye unguwar da misalin karfe 3 na dare, kuma suka bude wuta harbin kan mai uwa da wabi, bayan kowa ya gudu ne kuma suka kutsa kai cikin jami’ar.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce har yanzu babu tabbas game da adadin dalibai da malaman da ‘yan bidnigar suka tafi da su, amma dai ana kan bincike.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu