Isa ga babban shafi

Gwamnatin Zamfara za ta dauki mayakan sa-kai kusan dubu biyar

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da daukar jami’an tsaron sa kai na Civilian JTF guda 4200 a kokarin da ake yi na tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare
Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal Dare © The Guardian Nigeria
Talla

Amincewa da daukar jami’an tsaron na cikin batutuwan da suka fi shan chachaka a tsakanin ‘yan majalisar zartaswar jihar karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal Dare.

Da yake Karin haske mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris, ya ce bayan amincewa daukar jami’an tsaron, majalisar zartaswar ta amince da gina sabbi da kuma gyara wasu ajujuwa a makarantun gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar, ya ce za’a rarraba guraben aikin jami’an tsaron da za’a dauka cikin kananan hukumomi 14 na fadin jihar ta Zamfara.

Sanarwar ta ce za’a a baiwa kowaccce karamar hukuma guraben mutane 300 wadanda zasu shiga cikin aikin fatattakar ‘yan ta’adda, bayan sun karbin jerin horo da za’a basu.

A cewar sa za’a gyara tare da gina sabbin ajujuwa a makarantun karamar hukumar Gusau guda 49, sai Anka guda 11, sai guda 15 a karamar hukumar Bakura, akwai kuma guda 8 a karamar hukumar Bukuyyum da kuma guda 14 a birnin magaji.

Sauran sun hadar da guda 8 a kananan hukumomin Bungudu da Gummi, da guda 19 a karamar Kauran Namoda, sai 8 a Maru da 11 a Maradun, sai guda 8 a Talatar Mafara da kuma 27 a karamar hukumar Tsafe da wasu 11 a Zurmi sai guda 42 a shinkafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.