Kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan karar Nnamdi Kanu a watan Disamba
A Najeriya ,kotun kolin kasar ta sanya ranar 15 ga watan Disamba 2023 a matsayin ranar da zata yanke hukunci kan karar da ta shigar da ke neman tilastawa gwamnatin tarayya ta saki shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da ake tsare da shi yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba ne ,kotun kolin ta amince da shari’ar bayan da lauyan gwamnatin tarayya da Kanu suka cimma matsaya.
Tawagar lauyoyin gwamnatin tarayya ta kasance karkashin jagorancin mukaddashin daraktan daukaka kara na farar hula, a ma’aikatar shari’a ta tarayya, T.A. Gazzali, yayin da kungiyar lauyoyin Kanu ta kasance karkashin jagorancin tsohon babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Kanu Agabi. Duk da cewa Agabi ya jagoranci tawagar lauyoyin Kanu, Farfesa Mike Ozehkome ne ya gabatar da kara a gaban kotun koli.
Ozehkome ya roki kotun da ta ba da umarnin a gaggauta sakin wanda yake karewa daga tsare shi, da kuman neman gwamnatin tarayya ta biya shi kudade.
Idan za a iya tunawa, a wani mataki na bai daya da kwamitin mai mutane uku ya yanke, kotun daukaka kara ta yi watsi da tuhume-tuhume 15 na ta’addanci da gwamnatin tarayya ta shigar kan shugaban kungiyar IPOB.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu