Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Zaben Kaduna: Kotu ta yi watsi da shaidun PDP

Kotun Sauraron Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kaduna ta yi watsi da shaidun da Jam’iyyar PDP ta gabatar a karar da ta shigar na kalubalantar nasarar Gwamna Uba Sani na Jam’iyyar APC a zaben 2023.

Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani.
Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani. © Sen. Uba Sani X handle
Talla

Tun da farko alkalan kotun da ke zama a harabar Babbar Kotun Jihar Kaduna sun kori bukatun Gwamna Uba Sani da kan karar da PDP da dan takararta, Isah Muhammad Ashiru suka shigar na kalubalantar nasararsa.

Kotun ta yi watsi da shaidun na PDP da kuma hujjojin da suka gabatar a gabanta ne bisa hujjar cewa a lokacin da aka yi zaben, shaidun ba sa nan a rumfunan zaben da suke zargin an yi magudi.

Alkalan sun fara ne da yin watsi da bukatar Uba Sani da APC na neman ta kori karar da PDP da Isha Ashiru suka shigar.

Uba Sani da APC sun gabatar da bukatar ce bisa hujjar cewa sai da wa’adin kwana 21 da dokar zabe ta bayar na shigar da karar zabe ya wuce kafin PDP da dan takararta, Isha Muhammadu Ashiru suka shigar da karar.

Sai dai a yayi da suke watsi da bukatar da alkalan kotun sun bayyana cewa PDP da dan takararta sun shigar da karar ne a ranar 10 ga watan Afrilu, bayan zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023. Don haka suka yi fatali da bukatar.

Alkalan sun kuma yi fatali da bukatar APC da Uba Sani na neman ta kori karar da PDP da Isah Ashiru suka shigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.