Isa ga babban shafi

Napoli na shan suka bayan wallafa bidiyon shagube ga dan wasa Osimhen

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli a gasar Serie A, na shan chachaka daga magoya baya, bayan da ta wallafa wani gajeran bidiyo a shafin ta na Tiktok wanda a ciki kuma ake yi wa dan wasan Najeriya Victor Osimhen shagube, bayan da ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen
Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen AP - Fabio Ferrari
Talla

Osimhen wanda shi ya fi kowa zurawa kungiyar kwallaye a kakar da ta gabata, ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron ragar da ya samu a wasan da kungiyar ta Buga da Bologna a ranar Lahadin da ta gabata.

Jim kadan bayan zubar da kwallon ne, mai horas da kungiyar ya sauya shi da dan wasa Giovanni Simeone, ana saura mintuna hudu a tashi wasa, abinda da alamu bai yiwa Osimhen din dadi ba, har ma aka hango shi yana nuna rashin jin dadinsa ga mai horas da ‘yan wasa Rudi Garcia, kana kuma ya wuce zuwa benci.

Jim kadan bayan tashi daga wasan ne kuma, Osimhen ya yi amfani da shafin sa na Tiktok wajen neman afuwar mai horas da kungiyar da ma abokan wasasa, sakamakon barar da Fenarity din, sai dai a jiya Talata ne Club din ya yi amfani da shafinsa na Tiktok wajen ayyana Osimhen a matsayin mai kan kwakwa, da kuma yi masa shagube da ke nuna ya gaza zura wannan kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.