Isa ga babban shafi

Ba za mu sayar da Osimhen ba - Napoli

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Napoli, Aurelio De Laurentiis, ya ce ba zai sayar da Victor Osimhen ba a cikin kasuwar bazarar nan ta musayar 'yan wasa, a daidai lokacin da manyan kungiyoyi irinsu Bayern Munich da PSG da Manchester United da Chelsea da Arsenal ke rububin sayo shi.

Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen
Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen REUTERS - JENNIFER LORENZINI
Talla

Osimhen ya taimaka wa Napoli ta Italiya lashe kofin gasar Serie a karon farko cikin shekaru 33 bayan ya jefa kwallon canjaras a raga a karawarsu da Udinese a ranar Alhamis.

Yanzu haka shugaban na Napoli ya ce, yana da shirin ci gaba da rike zaratan 'yan wasansa har zuwa kaka mai zuwa kuma zai tsawaita kwantiragin kocin kungiyar Luciano Spalletti kamar yadda ya fadi.

Osimhen na kan gabar zama dan wasan Afrika na farko da ya lashe kyautar takalimin zinari a gasar ta Serie A sakamakon kwallaye 22 da ya jefa a wannan kaka.

Kazalika dan wasan ya goge tarihin da Samuel Eto na Kamaru ya kafa na yawan kwallaye 21 a kaka guda ta Serie A, sannan kuma ya yi kan-kan-kan da George Weah na Liberia wanda ya jefa jumullar kwallaye 46, kwallaye mafi yawa da wani dan Afrika ya jefa a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.