Isa ga babban shafi

Faransa ta tallafawa 'yan gudun hijirar Najeriya da Yuro miliyan 7

A dai dai lokacin da ake neman mafita kan halin da miliyoyin mutane ke ciki na yunwa da karancin abinci mai gina jiki a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, Gwamnatin kasar Faransa ta bada gudumowar Euro milyan 7 don tallafawa wadanda ke cikin mawuyacin hali. 

Sansanin 'yan gudun hijira na Jere da ke garin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Sansanin 'yan gudun hijira na Jere da ke garin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. AP - Chinedu Asadu
Talla

Najeriya dai ta dauki tsawon shekaru sama da 10 tana fama da rikicin mayakan Boko Haram, abin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, tare da asarar rayukan dubbai.

Rikice-rikicen mayakan dai ya fi shafar mata da kuma kananan yara, wadanda ssuka kasance masu rauni.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Bilyaminu Yusuf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.