Isa ga babban shafi

Buhari ya nemi afuwar 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roki jama’ar kasar da su masa aikin gafara idan ya saba musu a cikin shekaru 8 da yayi yana mulkinsa wanda ke kawo karshe a watan gobe. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2022 © Presidency
Talla

Buhari ya nemi gafarar ce lokacin da mazauna birnin Abuja suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a fadar gwamnati, inda ya bukaci yafiya idan ya sabawa wani yayin gudanar da aikinsa. 

Shugaban ya kuma godewa jama’ar kasar saboda yadda suka yi ta jurewa gwamnatinsa a shekarun da suka gabata, inda yace ziyarar Barka da Sallar ta bashi damar gabatar musu da godiyarsa da kuma yi musu ban kwana ganin cewar a watan gobe zai sauka daga karagar mulki. 

Buhari ya shaidawa mazauna Abujan cewar ya shirya yadda zai nesanta kansa da birnin da zaran ya bar karagar mulki, saboda burinsa na mulki ya cika, abinda zai bashi damar komawa mahaifarsa domin yin ritaya. 

Shugaban yace Allah ya bashi gagarumar dama wajen yi masa gwamna da minista da kuma shugaban kasa har sau biyu, saboda haka ya gode masa domin cimma burinsa na rayuwa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.