Isa ga babban shafi
Najeriya - Legas - Abuja

Tarwatsa masu zanga-zangar June 12 bai saba ka'ida ba - 'Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce babu wata doka ko hakkin da ta take sakamakon matakin da ta dauka na amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa gungun masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar da suka yi tattaki a jiya Asabar domin tunawa da ranar Dimokaradiyya.

Jami'an 'yan sandan Najeriya a birnin Abuja yayin kokarin watsa taron masu zanga-zangar ranar Dimokaradiya ta June 12. 12/6/2021.
Jami'an 'yan sandan Najeriya a birnin Abuja yayin kokarin watsa taron masu zanga-zangar ranar Dimokaradiya ta June 12. 12/6/2021. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ware kowace rana ta 12 ga watan Yuni ne a matsayin ranar Dimokaradiyyar kasar domin tunawa da kuma girmama marigayi MKO Abiola da gwamnatin sojoji soke nasarar zabensa a matsayin shugaban kasa a makamanciyar ranar a shekarar 1993.

Wasu ‘yan Najeriya sun yi amfani da damar bikin ranar ta dimokaradiiya wajen gudanar da zanga-zanga a wasu biranen kasar, inda a Abuja da Legas ta kai ga ‘yan sanda sun watsa taron nasu ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa, abinda ya janyo caccaka daga ‘yan adawa da kuma masu faftukar kare hakkin dan adam da suka ce hakan ya sabawa doka.

Sai dai akkakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya ce matakin ‘yan sandan yayi daidai da dokokin kasa da kasa da suka basu damar tarwatsa tarukan da ka iya rikidewa zuwa tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.